7 Oktoba 2019 - 05:26
​Kasashe Ukku Wadanda Kogin Nilu Ya Ratsa Su Sun Kasa Fahintar Juna

Gwamnatin kasar Masar ta bada sanarwan cewa taron tattaunawa tsakanin kasashen Masar, Sudan da kuma Habasha dangne da aikin gina madatsar ruwa ta Annahdah a cikin kasar Habasha kan kogin Nilu ya tashi ba tare da bangarorin ukku sun fahinci juna ba.

(ABNA24.com) Gwamnatin kasar Masar ta bada sanarwan cewa taron tattaunawa tsakanin kasashen Masar, Sudan da kuma Habasha dangne da aikin gina madatsar ruwa ta Annahdah a cikin kasar Habasha kan kogin Nilu ya tashi ba tare da bangarorin ukku sun fahinci juna ba.

Shafin yanar gizo na labarai mai suna, “Misril Yaum” ya nakalto Muhammad Sabbaa’ii kakakin ma’aikatar ruwa da noman rani na kasar Masar yana fadar haka a birnin Khartun babban birnin kasar Sudan, inda aka gudanar da tattaunawan.

Labarin ya nakalto Sabbaa’ii yana cewa gwamnatin kasar Habasha ta gabatar da wata sabuwar shawara kan batun madatsar ruwan wacce ta rushe dukkan yerjejeniyoyin da aka cimma a baya tsakanin kasashen ukku dangane da madatsar ruwan.

Kakakin ma’aikatar ruwa na kasar ta Masar ya kara da cewa kasar Masar tana bukatar shiga tsakani na manya-manyan kungiyoyin kasa da kasa kamar MDD don warware matsalar madatsar ruwan.

Amma ministocin ruwa na kasashen Sudan da Habasha wato Yasir Abbas da kuma Salshi Qabl sun ce babu bukatar shigo da wani tsakanin kasashen 3, don kwararrun da suke da su suna iya warware dukkan matsalolin da ake fuskanta dangane da madatsar ruwan.

Mutanen kasar Masar suna samun kashi 90% na ruwan da suke bukata ne daga dagakogin Nilu, don haka ne gwamnatin kasar take da sabani mai tsanani da kasar Habasha kan yadda sarrafa ruwan kogin bayan an kammala ginin madastar ruwan ta Annahdah.



/129